MENENE TERMUX? SHIN ZA'A IYA YIN HACKING DA TERMUX? YADDA AKE INSTALL NA HACKING TOOLS A TERMUX

Assalam yan'uwa mabiya wannan Shafi mai albarka, muna kara gaisuwa a gareku, kar Na cikaku da surutu, darasinmu na yau zamuyi shine akan

TERMUX


Kamar yadda darasinmu daya gabata, muka tattauna akan HACKING mutane da yawa suna tambayar akan za'a iya yin hacking da android, tayaya zasu mayar da wayarsu hacking machine, wannan application ne masu kyau Na hacking a wayar android, to Idan ka kasance acikin masu wannan tambaya, to ka karanta wannan darasin.
Amsar tambayar ku itace, EH za'a iya hacking da wayar android, kuma akwai application masu tarin yawa da zamu iya amfani da su, yanzu zan dauki daya daga ciki mu tattauna akai, Wanda zamuyi magana akansa shine termux

  1. menene Termux
  2. ya ake aiki da termux
  3. menene command a termux
  4. za'a iya amfani da termux wajen yin hacking
  5. ya ake installing Na hacking tools a termux


1..MENENE TERMUX

Termux shine [ Linux terminal emulator ] application ne domin wayoyin android, terminal emulator wani program ne da zaiba user damar shigar da command, acikin graphical environment, duk dalibin computer yasan [ command line interface ] da Shell.
A takaice Termux wani application ne Wanda zai baka dama kayi install na Linux packages a wayar ku android,
Ta hanyar amfani da wannan application mai suna Termux, zamu iya install Na Shell, Phyton,C,C++,Perl,ruby,java, da sauran package masu amfani
Kuma da taimakon Termux zamu iya, amfani da hacking tools masu yawa a wayar mu kamar Nmap,Hydra,sqlmap,Tool-x, da dai sauransu domin aiki da termux dole muna bukatar COMMANDs

2.. MENENE COMMANDS

a gurguje Idan akace termux commands, shine terminal command, ma'ana umarnine da ake rubutawa domin gudanar da wani keban taccen aiki, shi kuma wannan command din yana kama da Linux command,misali Zamu gwada amfani da Cmatrix effects, Idan muka bude termux dinmu sai mu rubuta < pkg install cmatrix > sai mu dannan enter, bayan haka sai mu rubuta cmatrix shikenan zamuga Cmatrix ya bayyana a termux, kamar haka.
wannan shine misalin command, akwai command masu trin yawa zamu shirya darasi musamman akan command, Idan kun fahimci command Zamuje bayani na gaba

3.. AMFANI DA TERMUX WAJAN HACKING


Dafarko muyi download na termux a playstore sai muyi install sannan mu budeshi, koda wayarka da rooting ko babu rooting zai aiki, bayan mun budeshi zamuga fili kamar haka

To sai mu rubuta

apt update && apt upgrade
sai mu danna enter, bayan ya gama update,sai mu danna

Termux setup storage
shikenan yanzu zamu gwada install na,
RED_HAWK tools

Red_hawk tools ne na information gathering an rubutashine da da php domin yin install dinshi sai mu danna

pkg install php
sai mu danna enter mudan jira bayan yagama sai mu dannan

pkg install git
sai mu danna enter shima bayan ya gama sai git clone

git clone https://github.com/tuhinshubra/RED_HAWK.git
shima sai mu danna enter danna wannan domin nemo directory nashi

Cd
danna enter sannan

ls
dannan enter sai

chmod +x RED_HAWK
dannan enter wannan

CD RED_HAWK
wannan enter

Chmod +x rhawk.php
shikenan yanzu munyi installing na RED_HAWK tools
sai ku karanta darasi Na gaba domin jin yadda ake aiki dashi, dama wasu hacking tools din,

naku har kullum Ibrahim kodamekazo gnm

Domin tambaya ko Karin bayani sai kuyi comment, domin tuntuba ta kasuwanci, zaku iya Neman mu a wanna number
kira ko WhatsApp 09067511830
mungode

Post a Comment

2 Comments

Anonymous said…
Aslm me gida muna godiya da iri wadann darusa amma oga a taimaka a yi mana video akan wanna darasin mungode
Yusuf umar muktar said…
Aslm me gida muna godiya da iri wadann darusa amma oga a taimaka a yi mana video akan wanna darasin mungode